Mahajjatan bana sun amfana ragowar Dala 410 daga kudin masaukinsu.

Mahajjatan bana sun amfana ragowar Dala 410 daga kudin masaukinsu.

Hukumar Aikin Hajji ta kasa ta bayyana cewar Mahajjatan bana sun amfana da ragin Dala 410 a kudin masaukinsu a kasar Saudiyya.
Shugaban Hukumar Alhaji Zikrullah Hassan ya bayyana haka a wani taron musayar ra’ayi da manema Labarai a ranar Lahadi a Legas.
Ya yi bayanin cewar Hukumar ta sami damar rage kudin masauki a Makkah daga Dala 930 zuwa Dala 520 a kan kowane mahajjaci a aikin Hajjin bana da ya gudana.
Zikrullah ya kara da cewar Hukumar ta kuma sami damar rage yawan kwanakin da mahajjata suka yi a Saudiyya.
A cewarsa, Hukumar ta sami damar shirya yin jigilar Alhazai zuwa gida Nijeriya da wuri ba kamar yadda ake yi ba a baya duk da cewar tana da kurarren kwanaki na kasa da wata daya ta kammala shirye-shiryen aikin.
Don haka ne ma ya fanganta babban kalubalen da Hukumar ta fuskanta a kan rashin jirgin sama na kasa da zai yi jigilar Alhazai zuwa da dawowa daga Saidiyya.
Zikrullah Hassan ya bada tabbacin cewar Hukumar ta fara gudanar da shirye-shiryen aikin Hajjin 2023 domin shawo kan matsalolin da ta fuskanta a bana.
Shugaban ya kuma bayyana wani shiri da Hukumar ke yi domin inganta tsarin ajiyar kudin aikin Hajjin, domin taimakawa maniyyata su ajiye isassun kudin da zasu biyawa kansu bukatar sauke farali.
Ya bayyana cewar kasashe irin su Malaysia da Indonesia na gudanar da irin wannan tsarin shekaru da dama da suka shude, inda suka sami damar samun rarar da ta basu damar rage kudin aikin Hajji.
Ya kuma yi bayanin cewar Hukumar na neman shawarwari a kan gyaran wasu sassan dokar Hukumar domin samun damar gudanar da aikinta cikin nasara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *