Mutane 7 suka mutu sanadiyyar konewar wata motar haya a Legas.

Mutane 7 suka mutu sanadiyyar konewar wata motar haya a Legas.

Hukumar bada agajin gaugawa ta jihar Legas, wato LASEMA tace fasinjoji bakwai ne suka suka kone kurmus a cikin wata motar haya da ta kama da wuta a Iyana Gworo jihar Legas.
Babban Sakataren hukumar LASEMA Dokta Olufemi Oke-Osanyintola, wanda ya tabbatar da hakan a wata sanarwa, ya danganta afkuwar hakan da tukin gangancin da Direban motar da ke dauke da fasinjoji 14 mai lamba KJA 699 GY, wanda bincike ya nuna cewar sanadiyyar hakan ya jaza motar ta kama da wuta inda daga cikin fasinjojin maza bakwai da mata biyu da kuma wani yaro suka kone kurmus.
Sanarwar ta bayyana cewar Direban bai mutu ba, sai dai ya sami konewa a wasu sassan jikinshi, yayin da aka ceto mata uku aka kuma yi hanzarin kaisu Babban Asibitin Gbagada.
Sanarwar ta kara da cewar jami’an Hukumar da kuma jami’an LASAMBUS ne suka mika gawarwakin ga Sashen kula da lafiya na jiha.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *