Uwargidan Shugaban Kasa Aisha Buhari ta yi kiran da a Ilimin ‘ya’yan talakawa goyon baya.

Uwargidan Shugaban Kasa Aisha Buhari ta yi kiran da a Ilimin ‘ya’yan talakawa goyon baya.

Uwargidan Shugaban Kasa Aisha Buhari ta yi kiran da a rika bada goyon baya ga samun Ilimin ‘ya’yan talakawa da tallafawa ‘ya’yan a masu karamin karfi a kasar nan.
Ta bukaci goyon bayan ne a ranar Asabar lokacin taron gudanar da neman gudunmuwa na wata Gidauniyar MA’ARUF da Matar Gwamnan jihar Yobe ta assasa aka gudanar a Abuja.
Wakiliyar Uwargidan Shugaban Kasar a wajen taron, Matar Babban Hafsan Sojojin kasar Misis Salamatu Yahaya ta jinjinawa kokarin wadda ta assasa Gidauniyar domin tallafawa masu karamin karfi a jihar Yobe.
Ta bayyana kokarin Gidauniyar ta fuskar gudanar da ayyuka a fannonin Ilimi da samar da tallafin bunkasa sana’a da kuma samar da ayyukan kula da Lafiya, wanda hakan yake tallafawa kokarin gwamnati da ma Kungiyar da Uwargidan Shugaban Kasa ta assasa mai suna Future Assured Foundation a Turance wajen gudanar da ayyukan jin kai ga al’ummar kasar nan.
Don haka ne ta yi roko ga masu ruwa da tsaki da su hada hannu wajen tallafawa Gidauniyar domin samar da sauki ga mata da kananan yara a jihar Yobe.
Aisha Buhari ta kuma bayyana irin ayyukan jin kai da Kungiyarta ta Future Assured ta gudanar a yankin Arewa maso Gabashin kasar nan ta fuskar samar da aikin yi da kula da Lafiya da kuma tallafawa mata da kananan yara.
Daga nan sai ta taya wadda ta assasa Gidauniyar MA’ARUF murna dangane da kyakkyawar kirkirar da ta yi, sannan ta roketa arzikin ganin dorewar Gidauniyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *