Jam’iyyar APC na ta karbar ‘Yan Jam’iyyun PDP da SDP a jihar Oyo.

Jam’iyyar APC na ta karbar ‘Yan Jam’iyyun PDP da SDP a jihar Oyo.

A ranar Asabar ce da yawan magoya bayan Jam’iyyun Siyasa a jihar Oyo suka canza shekarsu zuwa Jam’iyyar APC.
An karbi wadanda suka canza shekar a lokacin gudanar da wani taron ta shirya a wata makaranta dake yankin Ona-Ara a jihar ta Oyo.
Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya ya ruwaito cewar dan takarar Gwamnan jihar a APC Sanata Teslim Folarin tare da dan takarar Majalisar Dattawa a Shiyyar Oyo ta tsakiya Dokta Yunus Akintunde sune suka karbi wadanda suka canza shekar.
Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya ya kuma bada rahoton cewar Mogaji Akinjide ne ya jagoranci wadanda suka canza shekar daga PDP, yayin da Dattijo A Kalejaye ya jagoranci wadanda suka canza shekar daga SDP zuwa APC.
Shugaban Hukumar kula da Cacar Lottery Alhaji Fatai Ibikunle ya karbi wadanda suka canza shekar zuwa APC a madadin dan takarar Gwamnan jihar Sanata Folarin.
Ibikunle ya basu tabbacin nuna masu adalci da daidaito a cikin Jam’iyyar tare da yi masu alkawarin cewar zasu amfana da kulawa ba tare da nuna bambanci ba.
Ya horesu da su tashi tsaye wajen gudanar da aiki tukuru domin samar da nasara ga Jam’iyyar APC a baban zabe mai zuwa.
Akinjide wanda ya jagoranci wadanda suka canza sheka daga PDP zuwa APC yace sun yaba da yadda aka amshesu, shiko Kalejaye wanda ya jagoranci wadanda suka canza sheka daga SDP zuwa APC ya bayyana cewar sun canza shekar ne zuwa APC sakamakon kokarin da Sanata Folarin yake yi tare da yadda ya fito a matsayin dan takarar Gwamnan jihar.
Ya bayyana cewar samun nasara ga APC wata dama ce da al’ummar Karamar hukumar Ona-Ara da jihar baki daya zasu amfana.
Shiko dan takarar Gwamnan jihar Sanata Folarin, kira ya yi garesu da su koma mazabunsu daban-daban tare da halartar tarukan Jam’iyyar kodayaushe domin su san halin da Jam’iyyar ke ciki.
Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya ya bayyana cewar Kolawole Waliyu da aka fi sani da IKOKO da kuma Alhaji Amidu Olapade na daga cikin wadanda suka canza shekar zuwa Jam’iyyar APC.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *