Gwamnatin jihar Kano ta jaddada zimmarta ta kawo karshen shan miyagun kwayoyi

Gwamnatin jihar Kano ta jaddada zimmarta ta kawo karshen shan miyagun kwayoyi.
Gwamnatin jihar Kano ta sha alwashin gudanar da yaki a kan sha da dafarar miyagun kwayoyi tsakanin mata da matasa a fadin jihar.
Kwamishinar Harkokin Mata da Bunkasa jin Dadi Dokta Zahra’u Muhammad Umar, wadda ta bayyana haka a bikin horaswa da kuma gyara halayen matasan da suka tuba da dabi’ar shan miyagun kwayoyi a Cibiyar Gyaran Hali dake Karamar hukumar Kiru a jihar Kano.
Kwamishinar ta bada tabbacin cewar za a sami raguwar shan miyagun kwayoyi tare da samar da guraben aikin da ba zasu sami damar yin tunanin shan miyagun kwayoyi ba.
Dokta Zahra’u tace matasa 21, maza 20, da mace daya ne aka daidaita rayuwarsu tare da horas da su a kan dubarun sana’oi daban-daban domin su zamo masu dogaro da kansu.
Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya ya yi rahoton cewar an horas da matasan sana’oin yin takalma da aikin Kafinta da kiwon Kaji da kuma Dinkin Keke.
An raba masu Kekunan Dinki da kayan aikin Kafinta da na yin takalma da kayan yin Jikkuna da Kajin Kiwo da Kejin Kiwon Kajin da kayan sana’ar Walda da kuma Naira Dubu 20-20 ga kowanensu a matsayin kudin zirga-zirga.
Shugaban Karamar hukumar Alhaji Muntari Kafin Makyaki yace Cibiyar ta daidaita rayuwar dubban matasa tun lokacin da aka kafata.
A cewarsa, kafa Cibiyar ya jawo daukakar rayuwar Jama’a ta hanyar raguwar shan miyagun kwayoyi tsakanin matasa a yankin, don haka ne ma ya yi kira ga wadanda suka amfana da suyi amfani da kayan sana’ar da suka samu.
Da yake jawabin godiya a madadin wadanda suka amfana Aliyu Muhammad ya gode tare da yabawa gwamnati a kan karamcin da aka yi masu, sannan ya yi alkawarin cewar zasu yi amfani da kayan sana’ar da suka samu a kan hanya madaidaociya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *