Dan takarar Gwamnan jihar Katsina a PRP ya kalubalanci sauran ‘Yan takara da su je a yi masu gwajin shan miyagun kwayoyi

Dan takarar Gwamnan jihar Katsina a PRP ya kalubalanci sauran ‘Yan takara da su je a yi masu gwajin shan miyagun kwayoyi.

Dan takarar Gwamnan jihar Katsina a Jam’iyyar PRP Alhaji Imran Ja’afaru Jino ya kalubalanci sauran’Yan takara a jihar da su gabatar da takardar shedar cewa an yi masu gwajin basu shan miyagun kwayoyi ga al’ummar jihar.
Ja’afaru Jino, wanda ya yi kalubalen yayin da yake baje-kolin takardar shedar aikata hakan a gaban manema Labarai a ranar Asabar a Katsina, yace abu ne mai muhimmanci ga dukkan ‘yan takara su je a yi masu gwajin.
Ya bayyana cewar shi ya je an gwada shi a Hukumar Yaki da Hana sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta kasa, inda kuma Hukumar ta tabbatar da shi a matsayin wanda ba ruwanshi da tu’ammali da miyagun kwayoyi.
Ya kara bayyana cewar baya ga Hukumar NDLEA, Hukumar Babban Asibitin Katsina ma ta bashi takardar shedar tabbacin hakan.
Don haka nema ya tunasar da al’ummar jihar Katsina cewar tuni hukumar NDLEA ta yi kira ga ‘yan takara da su je a yi masu gabatar da kansu a yi masu wannan gwajin, amma suka bijirewa kiran.
Daga nan sai ya tabbatarwa al’ummar jihar Katsina cewar idan aka zabe shi, ya yi wani shirin ciyar da jihar zuwa wani matakin ci gaba wanda zai kai jihar ta yi gasa da duk wani birni a duniya dangane da ci gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *