Shugaba Muhammadu Buhari ya yabawa ‘yan Nijeriya mazauna kasashen waje.

Shugaba Muhammadu Buhari ya yabawa ‘yan Nijeriya mazauna kasashen waje.

Shugaba Muhammadu Buhari ya yabawa ‘yan Nijeriya mazauna Amurka a kan kyakkyawar dabi’ar da suke nunawa a wuren gudanar da huldodinsu daban-daban.
Ya yi kira garesu da su ci gaba da nuna hakan domin samun girmamawa daga masu masaukinsu.
Hadimin Shugaban Kasar a fannin yada Labarai Mista Femi Adesina ya bayyana hakan a wata sanarwar da ya sanyawa hannu, inda yace Shugaban Kasar ya yi yabon ne ranar Asabar a New York a wajen wani zauren tattaunawa da ‘yan kasar nan dake zaune a Birnin na New York.
Shugaban Kasar yace abin yabawa ne a gareshi ya ga da yawan ‘yan Nijeriya dake zaune a Amurka sun ci gaba da zamowa masu fice a wajen ayyukansu wanda har ya sanya Shuhaba Joe Biden ya nada wasu a cikin gwamnatin kasar.
Don haka ya yi fatar kowanensu zai kasance mai bin doka da oda a lokacin da suke zaune a Amurka.
Shugaban Kasar ya yabawa Shugabar Hukumar kula da ‘yan Nijeriya mazauna kasashen waje Misis Abike Dabiri Edewa a kan kirkirar shirye-shiryen dake jawo mazauna kasashen waje kusa da gida Nijeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *