Hukumar NSCDC ta biya Kudaden ariyas na shekaru shidda.
Babban Kwamandan Rundunar Tsaro ta Farin Kaya,wato NSCDC Dokta Ahmed Audi ya bayyana cewar tsarin kula da jin dadin Jami’an Rundunar zai ci gaba da samun kulawa ta Mussamman a karkashin jagorancinsa.
Kwamandan, wanda ya furta hakan a wani, zauren tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya ya shirya a Abuja, yace rundunar zata biya tariyas ga jami’anta da aka yi wa karin girma tsawon shekaru 6 da ba a basu ba.
Ya bayyana cewar Shugaban Kasa ya amince da a biya Kudaden ariyas na shekaru 4, wanda aka biya a halin yanzu, sauran na shekaru 2.
Ya kara da cewar yanzu ana jiran amincewar biyan ssuran kudaden ariyas na shekaru 2, inda yace da zarar an sami cikon, za a biya wadanda abin ya shafa.
Kwamandan ya ci gaba da cewar rundunar ta bullo da wasu shirye-shiryen samar da gidaje ga jami’anta.
Ya bayyana cewar rundunar ta fara biyan Kudaden Inshora ga jami’anta da suka sami raunikan da suka nakasa su kwata-kwata sanadiyyar hadari.
Kwamandan bai gushe ba sai da ya kara bayyana cewar an fara biyan diyya ga iyalen jami’an rundunar a karkashin tsarin Inshora, inda yace a yanzu rundunar ta biya Naira Miliyan 200 ta hannun Ofishin Shugaban Ma’aikatan gwamnatin tarayya wanda ba a yi ba tsawon shekara 7 da suka wuce.