‘Yansandan kasar Australia sun kwace kunshin miyagun kwayoyi.
Jami’an ‘Yansandan kan iyakar kasar Australia sun kwace kunshin miyagun kwayoyi da darajarsu ta kai Dollar kasar Miliyan 182 kimanin Dalar Amurka 121 da aka boye a cikin buhunan Kofi da aka yi niyyar shigowa dasu ta jirgin ruwa.
Haramtacciyar safarar da ta kunshi kilogiram 200 na miyagun kwayoyi da kilogiram shidda na hodar ibilis da aka bankado a lokacin da ta iso Melbourne daga Panama.
Tun farko farkon wannan makon jami’an tsaro a Melbourne suka bincika wani sunduki shake da lodin Kofi da aka yo safararshi ta jirgin ruwan daukar kaya inda suka gano wannan abin al’ajabi.
A cewar jami’an, da suka bincika, sai suka tabbatar da cewa miyagun kwayoyi ne da kuma hodar ibilis.
Suka ce idan da kunshin ya shiga titunan Australia, za a iya cefanar da miyagun kwayoyin a kan tituna 2,000,000, yayin da za a iya cefanar da hodar ibilis din a kan tituna 30,000 na kasar.
Har ila yau, Sufuritandan Tawagar binciken haramtattun gungun batagari na kasar McArthur ya bayyana cewar bankado miyagun kwayoyin alama ce ta yadda masu safarar miyagun kwayoyi ke amfani da wata dama ta shigowa da miyagun kwayoyi kasar Australia.