Hukumar NDLEA zata hada hannu da masu ruwa da tsaki wajen yaki da shan miyagun kwayoyi.

Hukumar NDLEA zata hada hannu da masu ruwa da tsaki wajen yaki da shan miyagun kwayoyi.

Kwamandan Rundunar Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi na Kaduna Umar Adoro ya fara gudanar da rangadin neman shawarwari ga al’umma domin neman goyon bayansu ta fuskar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi.
Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya ya ruwaito cewar Adoro ya ziyarci fadar Dagacin Anguwar Makera da Hakimin Gonin Gora a cikin Karamar hukumar Chikun.
Ya bayyana cewar ziyarar ta zama wajibi domin samun bayanan farko a kan halin da al’umma ke ciki game da shan miyagun kwayoyi.
Kwamandan ya bayyana cewar tsakanin watan Janairu zuwa Agusta, hukumar ta kama ton 10 na miyagun kwayoyi a jihar.
Don haka ne ma ya roki dukkan masu ruwa da tsaki su ci gaba da bada goyon bayansu ga Hukumar ta samar da ingantaccen bayani a kan masu safarar miyagun kwayoyi domin dakile su.
Kwamandan ya shaidawa Sarakunan cewar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ba hakkin jami’an tsaro bane kadai aiki ne da ya shafi al’umma.
Adoro ya yi kira ga matasa da akoyaushe su rungumi sana’a mai amfani da zata zamo mai amfani ga al’umma.
Sarakunan sun yaba da ziyarar tare da jinjinawa hukumar NDLEA a kan nasarorin da take samu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *