Nijeriya ce kasar sha’awar zuba jari a yankin Afirka ta Yamma.

Nijeriya ce kasar sha’awar zuba jari a yankin Afirka ta Yamma.

Gwamnan jihar Kebbi Atiku Bagudu ya bayyana hakan a lokacin da ya karbi bakuncin Shugaban Kamfanin samar da Shinkafa na WACOT Muhammad Lawal Birnin Kebbi.
Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya ya ruwaito cewar Gwamna Bagudu ya bayyana cewar Nijeriya ce ke rike da kambin zama kasar da tafi ban sha’awar zuba jari a yankin Afirka ta Yamma da sauran sassan duniya.
Ya kawar da duk wani haufin cewar manoman Shinkafa a Nijeriya zasu iya rubanya amfanin Shinkafar da suke samu idan suka rika amfani da dubarun noma na zamani wanda ya bayyana a matsayin wajibi a wannan zamani
Ya godewa Shugaban Kamfanin WACOT a kan goyon bayan da yake ba manoma na samar masu da ingantaccen irin Shinkafa, sannan ya nuna jin dadinshi ganin yadda Kamfanin ya nuna cewa Nijeriya kasa ce da ta zamo abin sha’awar zuba jari.
Bagudu ya yi nunin cewar Kamfanin Casar Shinkafa da WACOT ya kafa a Argungu wani tabbaci ne na cimma wannan gurin wanda ya kuma samar da dogaro da kai game da samar da Shinkafa a kasar
Tun farko saida Shugaban Kamfanin WACOT Muhammad Lawal Birnin Kebbi ya bayyanawa Gwamnan cewar sun kawo ziyarar ce domin domin tabbatar da samar da isasshen amfanin gona idan har suka sami tallafin bankuna.
Wani Jami’i daga jihar Legas Daraktan kula da farashin Shinkafa Mista Balogun Wakilu Olabode ya yabawa Gwamna Bagudu a kan aza harsashin farfado da noma Mussamman noman Shinkafa, wanda a halin yanzu irin Shinkafar da Gwamnan ya samar shine wanda jama’ar Legas suka fi kauna.
Itama Misis Habiba Suleiman Jami’a a Kamfanin WACOT ta gabatar da rahoton ci gaban da Kamfanin ya samu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *