Shugaba Muhammadu Buhari zai kaddamar da hadadden shirin INFF a New York.

Shugaba Muhammadu Buhari zai kaddamar da hadadden shirin INFF a New York.

A ranar Juma’ar nan ce ake sa ran Shugaba Buhari zai kaddamar da hadadden shirin kashe kudade na Nijeriya a Birnin New York domin ci gaba mai dorewa.
Mai magana da yawun Shugaban Kasa Mista Femi Adesina ne ya furta hakan a wata sanarwar da ya fitar a Abuja, inda ya bayyana cewar Shugaba Buhari zai kaddamar da shirin a Babban taron Majalisa Dinkin Duniya karo na 77 dake gudana a New York.
Adesina yace kamar yadda matakin da taron Addis Ababa ya dauka, hadadden shirin, wani shiri ne na dubarun yin amfani da kudi ta fuskar samar da ci gaba mai dorewa a matakin kasa.
A cewarsa, Shirin zai taimakawa masu gudanar da mulki samar da dubarun kara yawan hannun jari domin ci gaban kasar mai dorewa da jalauta kudade da kadarori ta fannin cimma nasarar samar da ci gaba.
Domin cimma nasarar aiwatar da shirin, yace Nijeriya ta kafa Kwamitin aiki da cikawa na Shirin wanda Ma’aikatar Kudi da Kasafin Kudi da Tsare-tsaren kasa zata shugabance shi da Ministar Ma’aikatar zata wakilta.
‘Yan Kwamitin sun hada da Gwamnan Babban Bankin Nijeriya da Shugaban Hukumar Tara Kudaden Shika na kasa da Shugaban Kungiyar Gwamnonin Nijeriya da Darakta Janar na Ofishin kula da Kasafin Kudi na Tarayya.
Sauran sune Darakta Janar na Ofishin kula da basussuka da Shugaban Hukumar Kididdiga na kasa da Babban Mataimaki na Mussamman ga Shugaban Kasa a kan Dorewar Muradun Karni da Babban Jami’in Majalisa Dinkin Duniya a Nijeriya da kuma Wakilin Shirin Bunkasa kasa na Majalisa Dinkin Duniya a Nijeriya.
Sauran sune Shugaban Tawagar Shirin dorewar gurin Kungiyar Tarayyar Turai da Wakilin Bankin bada Lamuni a Nijeriya da Daraktan Bankin Duniya dake Nijeriya da kuma hadakar shugabancin bangarorin bada shawara masu zaman kansu.
Adesina yace wadanda ake sa ran zasu halarci bikin kaddamarwar sun hada da wasu Shugabannin kasashe da Na’ibar Sakatare Janar ta Majalisa Dinkin Duniya Amina Mohammad da wakilan kasashe da na kungiyoyin kasa da kasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *