Fitaccen Dattijo kuma dan adawa a arewacin najeriya,kuma daya daga cikin dattijan kasar, ya bayyana cewa, zalunci ne ga kudancin muddin ‘yan arewaq suka nuna sha’awar sake neman shugabancin kasar bayan kamala wa’adin shugaba Buhari.
Ya bayyana nhaka e, a marnatin day a mayar bayan cecekucen masu ruwa da tsaki a harkokin siyasar kasar kan batun mulkin karba-karba tsakanin Arewa da kudu gabanin zaben Da ke tafe a shekarar 2023.
Yakasai ya kara da cewa, “duk da c ewa shi baya da katin daya daga cikin jam’iyyun kasar,zalunci ne ga kudu, idan’yan arewa suka nemi shugabancin kasa bayan karewar wa’adin shugaba Buhari a 2023.” Ya kara da cewa,“Ta yaya za a ce kullum mu ’yan Arewa ne za mu yi mulki? Babu adalci a wannan al’amari, mu mu yi mulki, su (Kudu) su yi mulki, wannan shi ne adalci.”
“Ina mamakin me ‘yan Arewa za su ce wa jama’a? Me za su nuna wa ’yan Najeriya cewa sun amfana ko za su amfana domin su ba da kuri’unsu?
“A cikin shekaru shida zuwa bakwai, me ‘yan Arewa suka yi? Wace nasara shugabanci ya cimma da ya taimaka wajen ci gaban kasa da tattalin arzikinta, ko wani ci gaba da taimakon al’umma?
“Wace babbar nasara ‘yan Arewa suke da ita da za su iya amfani da ita wajen yin kira ga sauran ‘yan Najeriya da su sake ba su kuri’u?’in ji shi.”
Yakasai ya ce, “sha’awarsa ta siyasa tun farko, ta kasance a kan adalci.”
A halin yanzu,wasu fitattun ’yan Arewa irin su tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar da tsohon Gwamnan Jihar Kano Alhaji Rabi’u Musa Kwankwaso da Gwamnan Jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal da tsohon shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki duk sun nuna sha’awarsu ta neman shiga zaben 2023.