Tsawa ta kashe mutane 21 a Gabashin India
Akalla mutane 21 ne suka mutu a jihar Bihar dake afkuwa Gabashin India sanadiyyar mamakon ruwan sama tare da tsawa da aka tafka a yankin har na tsawon sa’oi 24
A ranar Talata ce wani Jami’in hukumar kare afkuwar iftila’i a jihar ya bayyana cewar wadanda suka mutu manoma ne ko kuma masu aiki ne a wata gona da suke yin shuka ko kuma wani abu makamancin haka.
Ya bayyana cewar an sami rahoton mutuwarsu a kimanin yankuna 10 na jihar.
Jami’in ya bayyana cewar an sami rahoton mutuwar mutane hudu-hudu a yankunan Pumia da Araria, mutane uku daga yankin Supaul, mutane biyu-biyu daga yankunan Banka da Jamul da kuma Nawada, sai kuma a yankunan Begusarai da Sheikhpura da Saran da kuma Saharsa aka sami rahoton mutuwar mutum daya-daya.
Hakan ne ya sanya Babban Minista Nitish Kumar ya sanar da raba diyyar Rupees 400,00 daidai da Dalar Amurka 5,023 ga kowadanne iyalen mamatan.
Babban Ministan ya kuma bada shawara ga jama’a da su kasance masu lura da irin wannan yanayi kafin hakan ta faru.
A cewarsa, ya zama wajibi jama’a su rika bin umurnin Hukumar kare afkuwar iftila’i ta kasa domin kare kansu daga iftila’in tsawa ta hanyar kasancewa cikin gida a irin wannan yanayi.