Kotun Faransa ta daure ‘Yansanda 3 a kan kashe wani bakar fata a 2015

Kotun Faransa ta daure ‘Yansanda 3 a kan kashe wani bakar fata a 2015

A ranar Talata ce wata Kotun kasar Faransa ta sami wasu jami’an ‘Yansanda uku da laifin kashe wani bakar fata a Birnin Paris a 2015.
Kotun ta daure kowanensu tsawon shekaru 15.
Amadou Koume dan kimanin shekaru 33 ya mutu ne bayan da jami’an ‘Yansandan a wata nashaya suka bugashi da kasa sannan suka makareshi.
Kotun ta yi nazarin rashin tausayin da ‘Yansandan suka nuna da suka kifar da mutumin rub-da-ciki har fiye da mintuna shidda tare da bankare shi da kuma kargama mashi ankwa a hannuwanshi a jikin wani karfe.
A cewar ‘Yansanda, an yi la’akari a ofis6hin ‘Yansandan da aka kai shi cewar Koume na cikin mayen hodar ibilis a daren 6 ga watan Maris 2015.
Bayan an kammala auna lafiyarshi ne aka gano cewar ya kamu da wata matsalar da shan hodar ibilis din ta jaza mashi.
Alkalin Kotun ta zargi ‘Yansandan uku kan rashin bincikar lafiyar Koume duk da lalurar tabin hankalin da yake da ita.
Ta dora masu laifin gazawasu ta bincike, wanda hakan ya zamo silar mutuwarsa, hakan kuma ya tabbatar da aikata kisan kai suka yi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *