Mafarauta sun cafke wani mutum da kokon kan mutum a jihar Osun.

Mafarauta sun cafke wani mutum da kokon kan mutum a jihar Osun.

‘Yansanda a jihar Osun sun garkame wani dan kimanin shekaru 28 Ismail Adewuyi da aka samu tare da sabon datsattsen kai da hanjin wata mata a yankin Ede dake jihar.
Mai magana yawun Rundunar ‘Yansandan jihar SP Yemisi Opalola ta bayyana cewar wani Isa Usman dan Kungiyar Mafarauta ta Nijeriya ne ya cafke matsafin da ake zargin a ranar Asabar a wata Makabarta ya kuma mika shi ga ‘Yansanda.
Opalola ta bayyana cewar ‘Yansanda sun fara tuhumar wanda ake zargin domin samun karin wasu bayanai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *