Shugaba Muhammadu Buhari ya isa New York domin halartar babban taron Majalisa Dinkin Duniya.
Shugaba Muhammadu Buhari ya isa birnin New York domin halartar babban taron Majalisa Dinkin Duniya karo na 77.
Wakilin Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya a Majalisar ya bada rahoton cewar Shugaba Muhammadu Buhari ya sauka ne a filin jiragen saman kasa da kasa na JF Kennedy dake New York da misalin karfe 6:20 na Yamma.
Shugaban ya sami taryar Ministan harkokin wajen kasar nan Geoffrey Onyeama da Babban Wakilin Nijeriya a Majalisar Tinjani Muhammad Bande da Jakadan Nijeriya a Amurka Dokta Misis Uzoma Emenike.
Taron, wanda aka fara zama a ranar Laraba 13 ga watan Satumba zai tattauna ne game da lalubo dubarun magance babbar barazanar dake addabar ci gaban kasashe masu tasowa.
Manyan lamurran da zauren Majalisar ya tattauna a taron da aka gudanar a 2022 sun hada da yakin Rasha da Ukraine da rikita-rikitar dake fuskantar samar da makamashi da kuma kawo karshen annobar COVID-19.
Ana sa ran Shugaba Muhammadu Buhari zai halarci bikin bude wani babban taro a kan tattaunawa game da bunkasa harkar Ilimi a ranar Litinin, inda zai gabatar da jawabi a kan abin da ya shafi kasarsa ta wannan bangaren.
A ranar Laraba Shugaba Buhari zai halarci bikin bude wata gasar muhawara da Majalisar ta shirya, inda Shugaban Majalisar Csaba Koros da kuma Sakatare Janar Antonio Guterres zasu bude gasar.
A ranar Laraba har ila yau, Shugaba Buhari zai zamo na farko wajen gabatar da jawabin kasar nan ga Zauren Majalisar, wadda itace rana ta biyu ta gudanar da muhawar a Babban taron.
Akwai muhimman taruka daban-daban da Shugaba Buhari zai halarta tun daga ranar da ya isa har zuwa ranar Juma’a