Auren Wuri: Asusun UNICEF ya bukaci tilasci ga ilimin ‘ya’ya mata.

Auren Wuri: Asusun UNICEF ya bukaci tilasci ga ilimin ‘ya’ya mata.

Asusun UNICEF ya bukaci da a tilasta samar da Ilimi ga ‘ya’ya mata a matsayin wata kariyar da zata hana tilasta auren wuri.
Wakilin UNICEF a Nijeriya Mista Peter Hawkins ya furta hakan a lokacin da ya zamo bako na mussamman a wani shiri da Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya ya shirya a Abuja.
Hawkins, wanda ya bayyana cewar auren wuri ya zamo babbar matsala a kasar nan, ya yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki su lalubo wasu hanyoyin magance wannan dabi’ar domin ba yara mata damar kasancewa a makaranta.
Ya jaddada cewar karatun ‘ya’ya mata na daya daga cikin muhimman lamurran da UNICEF ta sanya a gaba domin muhimmancin da yake da shi ga lafiyarsu.
Ya kara da cewar Shirin samar da Ilimi ga yara mata na GEP da UNICEF ke gudanarwa an shirya shi ne da nufin wayar da kai a kan lamurran da suka shafi yara mata da kuma harkar Ilimi a kasar nan.
Daga nan sai Wakilin na UNICEF ya bada misalan shirye-shirye da UNICEF ta bullo da su domin ci gaban kasar nan, inda yace zasu taimakawa ‘ya’ya mata su sami Ilimi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *