Osinbajo ya sanya hannu a rajistar ta’aziyyar rasuwar Sarauniyar Ingila.

Osinbajo ya sanya hannu a rajistar ta’aziyyar rasuwar Sarauniyar Ingila.

A ranar Lahadi ce Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya sanya hannu a rajistar ta’aziyyar rasuwar Sarauniyar Ingila da aka aje a Fadar Lancaster dake Birnin London.
Babban Mataimaki na Mussamman ga Mataimakin Shugaban Kasa a fannin yada Labarai Laolu Akande ne ya bayyana haka a wata sanarwa.
Sanarwar ta nuna cewar Mataimakin Shugaban Kasa ya bayyana Marigayiya Elizabeth a matsayin wadda ta rungumi kowane jinsi dake fadin duniya.
Ya bayyana cewar Nijeriya ta bi sahun gwamnatin Biritaniya da al’ummar kasar da kasashe renon Ingila da sauran kasashen duniya wajen gabatar da ta’aziyyar rasuwar Sarauniyar Ingila ga gidan sarautar Ingila.
Farfesa Yemi Osinbajo ya kuma bi sahun sauran shugabannin kasashen duniya wajen gabatar da biyyayyarsu ta karshe ga Marigayiya Elizabeth a lokacin bizneta ranar Lahadi.
Daga bisani Mataimakin Shugaban Kasar ya gana da Sakataren harkokin wajen Ingila James Cleverly, inda suka tattauna lamurran da suka shafi diflomasiyya a kan yadda za a bunkasa yarjejeniyar kasuwanci tsakanin kasashen biyu.
Sun kuma tattauna a kan yadda za a karfafa harkar tsaro a yankin Sahel da kuma yankin Afirka baki daya.
Cleverly ya yabawa Nijeriya a kan yadda ta halarci bikin bizne gawar Sarauniya Elizabeth.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *