Jam’iyyar APC na kara karfafa a Karamar hukumar Goronyo.

Jam’iyyar APC na kara karfafa a Karamar hukumar Goronyo.

Yayin da ake ta shirin fara gudanar da yakin neman zaben mukaman siyasa daban-daban a kasar nan, da yawan magoya bayan jam’iyyun PDP da na NNPP na ta canza shekarsu zuwa Jam’iyyar APC a Karamar hukumar Goronyo dake jihar Sokoto.
A wata sanarwa da Daraktan Yada Labaru a shafukan sada-zumunta na zamani na Sanata Aliyu Magatakarda Wammako Bashar Abubakar ya sanyawa hannu ranar Asabar, ta bayyana cewar daga cikin wadanda suka canza shekar, sun hada da Alhaji Manniru Malami dan takarar Majalisar Dokoki ta jiha a Jam’iyyar NNPP tare da dukkan shugabannin Jam’iyyar na mazabu 11 na Karamar hukumar hadi da dukkan magoya bayan shi.
Karin wadanda suka canza shekar sun hada da wasu jiga-jigan Jam’iyyar PDP da suka hada da tsohon dan takarar Majalisar Dokoki ta jihar Alhaji Shehu Dan Tsamaye da Sakataren Kudin Jam’iyyar PDP Alhaji Hamza ‘Yar Dole da Shugaban Kungiyar Shugabannin Mazabu na yankin Alhaji Amadu Dan Kansila da kuma wani jigon Jam’iyyar PDP a yankin Alhaji Ya’u Isah Mai Alewa.
Da yake jawabi a lokacin da ya tarbi Dan takarar Gwamnan jihar Ahmad Aiyu Sokoto da sauran jiga-jigan Jam’iyyar APC Shugaban Jam’iyyar APC na Karamar hukumar Goronyo Alhaji Kabiru Sarkin Fulani ya bayyana cewar adadin magoya bayan PDP da NNPP 9,800 ne suka dawo Jam’iyyar APC.
A lokacin da yake karbar wadanda suka canza shekar, Shugaban Jam’iyyar APC na jihar Isah Sadiq Achida ya bada tabbacin cewar zasu ji dadin kasancewarsu a Jam’iyyar APC domin za a kare dukkan muradunsu kamar na wadanda suka iske a cikinta.
Shiko Dan takarar Gwamnan jihar Ahmad Aiyu Sokoto, bayyana jin dadi ya yi a kan ci gaban da aka samu tare da bayyana cewar hakan wata alama ce ta nuna samun nasara ga Jam’iyyar.
Wadanda suka yi jawabi daga cikin wadanda suka canza sheka zuwae APC sun hada da Dan takarar Majalisar Dokoki ta jiha a inuwar Jam’iyyar NNPP Alhaji Manniru Malami da Shugaban Jam’iyyar NNPP na Karamar hukumar Goronyo da Sakataren Kudin Jam’iyyar PDP a yankin Alhaji Hamza’Yar Dole da tsohon Kansilan PDP Habibu Shehu Rimawa da kuma Shugaban Kungiyar Shugabannin Mazabu na yankin Alhaji Amadu Dan Kansila.
Sun bayyana cewar Jam’iyyar PDP a jihar ta gaza samar da ababen more rayuwa tare da tsunduma Jama’a cikin kuncin talauci a tsawon shekaru bakwai da suka shude.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *