Wani Dan Majalisar Wakilai ya raba tallafin buhunan Shinkafa 278 ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a Kano.
Dan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Wudil da Garko Muhammad Ali Wudil ya rabar da buhunan Shinkafa 278 ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa bada dadewa ba a Karamar hukumar Wudil dake jihar Kano.
A lokacin rabar da tallafin, wakilin Dan Majalisar Alhaji Haladu Ishak yace bada tallafin na da nufin rage matsaloli ne ga wadanda ambaliyar ruwan ta shafa, inda ya bayyana cewar ambaliyar ruwan wadda ta shafi kauyuka tara kwanakin baya, ta jaza matsaloli ga mutane da dama, wanda bukatar tallafa masu ta zama wajibi.
A cewarsa yankunan da matsalar ta shafa sun hada da Kofar Yamma da Dugurawa da Dafawa da Tsibiri da Fangale da Gaban Komi da Gorubobi da Babilon da kuma Gandu.
Dan Majalisar, a cewar Wakilinsa ya damu matuka, don haka ne ya kafa wani Kwamitin Wakilai biyar su binciko mizanin barnar da ambaliyar ruwan ta yi.
Ya bayyana cewar duk wanda ambaliyar ruwan ta shafa zai amfana da tallafin Shinkafar, ya kara basu tabbacin cewar Ali Wudil ya gabatar da al’amarin ga Hukumar Bayar da Agajin Gaugawa ta kasa domin ta tallafa kuma har ta turo jami’anta domin auna yawan asarar da ta afku kafin ta gabatar da nata tallafin.
Daya daga cikin wadanda iftila’in ya shafa Salisu Ahmed Rufa’i ya godewa Ali Wudil a kan bayar da tallafin.
Shima Bayero Shu’aibu cewa ya yi tallafin ya zo a kan lokacin da ake bukatarshi.