Wata Tankar Mai ta kama da wuta a jihar Neja.
Rundunar Kiyaye Hadurra ta kasa ta bayyana cewar wata Tankar Mai ta kama da wuta a Kauyen Badeggi dake cikin Karamar hukumar Bida a jihar Neja.
Kwamandan Shiyya na Rundunar a jihar Mista Kumar Tsukwam ne ya shedawa Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya a ranar Lahadi a garin Minna cewar lamarin ya afku ne a ranar Asabar da misalin karfe 7:30 na dare.
Tsukwam yace Tankar na dauke da lodin man fetur ne zuwa Abuja inda ta rika yoyo wanda hakan ya sanya wuta ta tashi daga rumfar wani mai shayi har ta isa ga Tankar, inda nan take ta kama da wuta tare da wasu motoci guda biyu.
Kwamandan Shiyyar ya bayyana cewar matane hudu ne hadarin ya rutsa da su sai dai babu abin da ya same su.
Ya kara da cewar jami’an Rundunar ta RS7.24 dake Bida da jami’an kashe gobara da sauran jami’an hukumomin tsaro sun taimaka wajen shawo kan lamarin.
Don haka ne ma Kwamandan Shiyyar ya shawarci masu motoci da akoyaushe su rika kula da lafiyar motocinsu kafin da kuma in sun hau kan hanya.