Kungiyar’Yan Jarida ta gargadi ‘ya’yanta su guji hada baki da ‘Yan Siyasa.
Kungiyar ‘Yan Jarida ta kasa reshen jihar Sokoto ta gargadi membobinta da su guji kwadayin ‘Yan Siyasa yin amfani da su wajen bata sunayen wasu.
Kungiyar ta yi gargadin ne a wata sanarwar bayan taron da ta yi na Shugabanninta, da Shugaban Kungiyar na jiha Dalhatu Safiyal Magori da Sakatarenta Muhammad Bello suka sanyawa hannu.
Sanarwar bayan taron ta bayyana cewar ganin babban zaben 2023 na kara gabatowa, kamata ya yi ‘yan Kungiyar su kaucewa tsunduma cikin harkokin Siyasa domin su tabbatar da kwarin gwuiwar jama’a ta nuna adalci ga aikinsu.
Don haka ne ma Kungiyar ta yi gargadin cewar babu wani da zata ba kariya ga duk wanda ya yi karan-tsaye ko cin fuskar wani.
Taron ya kuma yi roko ga ‘yan siyasar kasar nan su tabbatar da gudanar da yakin neman zabe bisa lumana tare da tafiyar da lamurransu cikin tsanaki kafin da kuma bayan zabe.
Ta kuma yi kira ga gwamnatocin tarayya da jiha da su lalubo dubarun magance matsalar tsaro a jihar da kasar baki daya.
Taron har ila yau ya ba gwamnati shawarar hanzarta daukar matakin magance yawaitar gudun hijarar dake afkuwa daga yankunan karkara zuwa birane da karuwar barace-baracen kan tituna hadi da yawaita ‘yan gudun hijarar da rashin tsaro ya haddasa a kasar nan.
Taron ya kara kira ga gwamnatin jihar Sokoto da ta yi hanzarin kafa Ma’aikata ko Hukumar da zata kulawa da ‘yan gudun hijara don taimakawa a magance yawaitar barace-baracen kan titi a jihar.
Game da yajin aikin da Kungiyar ASUU kuwa, Taron ya roki gwamnatin tarayya da Kungiyar ASUU su yi karatun ta natsu ta fuskar samar da madogara tabbatacciyya.
Daga nan Taron ya yi kira ga wadanda suka yi rajistar zabe amma basu karbi katinun jefa kuri’a ba da su hanzar karbo katinunsu.