Kwamitin bunkasa zaman lafiya na kasa ya gayyaci jam’iyyun siyasa da’yan takarar kujerar Shugabancin kasar nan a zaben 2023 tare da masu magana da yawunsu domin sanya hannu a yarjejeniyar gudanar da yakin neman zabe mai tsafta
Takardar gayyatar da ta fito ranar Alhamis, a cewar Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya wato NAN, an gayyaci ‘yan takarar da masu magana da yawunsu ne a ranar 29 ga wannan watan ne a Babban dakin taro na kasa da kasa dake Abuja.
NAN ta ruwaito cewar a wata takarda da Shugaban Kwamitin Janar Abdulsalami Abubakar mai ritaya ya sanyawa hannu ta nuna cewar za a sanya hannun yarjejeniyar ne sau biyu kafin nan da babban zaben 2023.
Za a sanya hannu karon farko da an fara gudanar da yakin neman zabe a cikin watan Satumbar nan, karo na biyu na sanya hannun yarjejeniyar kuma a cikin watan Janairun 2023 kafin a gudanar da zabe.
Yarjejeniya ta farko a cewarsa, na da nufin ganin jam’iyyun siyasa da ‘yan takara da mukarrabansu sun gudanar da yakin neman zabe a shafukan sada-zumunta da kuma sarari cikin tsanaki ba tare da nuna wani bambancin da zai iya haddasa tashin hankali ko jawo fitinar rashin tsaro ga kasar nan ba.
Kamar yadda takardar ta nuna, manufar yarjejeniyar itace domin ganin an gidanar da yakin neman zabe a kan harkokin da suka shafi al’umma.
Wannan shiga tsakanin na da nufin tallafawa kokarin samar da zaman lafiya, domin kaucewa tashin hankali da kuma yin biyayya ga ka’idodi lafin da kuma bayan an bayyana sakamakon zabe.