Bankin Duniya ya ayyana cewar kasashen duniya zasu shiga halin matsin tattalin arziki a 2023

Bankin Duniya ya ayyana cewar kasashen duniya zasu shiga halin matsin tattalin arziki a 2023 sanadiyyar tsauwala riba da manyan bankunan kasashen ke yi sakamakon talaucin dake afkuwa.
Bankin Duniyar dai ya bayyana hakan a wani nazari da ya gudanar cewar manyan bankunan kasashen duniya nata tsauwala riba a hada-hadarsu a bana ba tare da tunanin abin da ya afku shekaru biyar da suka shude ba, dabi’ar da idan ba a yi hankali ba zata ci gaba da dorewa.
Nazarin da Bankin Duniyar ya yi la’akarin cewar masu saka jari na tsammanin manyan bankunan kasashe za su tsauwala riba zuwa kashi hudu cikin 100 a 2023, wanda ya zamo fiye da makin kashi biyu na gacin da suka samu a 2021.
Mai rikon mukin Mataimakin Shugaban Bankin Duniya a kan daidaiton bunkasar kasashe Ayhan Kose yace damuwarshi itace irin wannan dabi’ar zata wuce gona-da-irin da zata haddasa matsalolin da zasu kasance masu hadari ga al’umma a hada-hadar kasuwanci da kuma bunkasuwar tattalin arziki.
Don haka a cewarsa, idan ana son samun maslahar samun bunkasa, masu tafiyar da ragamar tsare-tsare na iya juyawar da fuskarsu zuwa bunkasa samar da abinci, ya kara da cewar kamata ya yi tsare-tsaren su samar da hurumin kara bunkasa jari da kuma inganta aiki wadanda suke muhimmai ne gabunkasar kasa da rage yunwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *