‘Yan Sanda Sun Cafke Likita Mai Yin Allurar Mutuwa, Ya Sace Motocin Marasa Lafiya.

‘Yan Sanda Sun Cafke Likita Mai Yin Allurar Mutuwa, Ya Sace Motocin Marasa Lafiya.

Ana zargin wani Likita a asibitin Kaiama da ke Arewacin jihar Kwara da laifin kashe marasa lafiyansa Idan Likitan ya kashe marasa lafiya ta hanyar allura, ya kan dauke motocinsu domin ya saida a kasuwa Dubun wannan mutumi da ake zargi ta cika bayan an gano wata mota da ya saida bayan ya kashe mai ita

Jami’an ‘yan sandan Najeriya na reshen jihar Edo, sun yi ram da wani likita da ake zargin yana da hannu wajen mutuwar wasu direbobin mota. Premium Times tace wannan likita mai suna Abbas Adeyemi yana yi wa marasa lafiya muguwar allurar da take yin kisa, domin ya sace motocinsu. Abbas Adeyemi mai shekara 36 yana aiki ne a babban asibitin garin Kaiama a jihar Kwara. Likitan ya amsa laifinsa, ya fadawa dakarun ‘yan sanda cewa ya sace motoci biyu daga hannun wasu marasa lafiyansa bayan ya tsira masu allura.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *