Karamar Hukumar Mubi ta Arewa ta raba tallafin kekukana guda 75 ga wasu jajirtattun ma’aikatanta

Majalisar Karamar Hukumar Mubi ta Arewa ta raba tallafin kekukana guda 75 ga wasu jajirtattun ma’aikatanta.
Shugaban Karamar hukumar Alhaji Suleiman Yahaya ya bayyana hakan ga Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya a garin Yola ranar Laraba.
Ya bayyana cewar an tallafawa Masinjoji da masu share-share da kekuna guda 35, yayin da aka rabawa kananan ma’aikatan dake aiki a Fadar Sarkin Mubi.
Yace yin hakan na da nufin samar masu da saukin zirga-zirga wajen zuwa aiki da kuma komawa gida bayan an tashi aiki, ya kara da cewar an tallafa masu ne kyauta ba biya.
Shugaban ya yi kira ga wadanda suka amfana da tallafin da su yi amfani da kekunan yadda yadda ya kamata tare da jaddada cewar za a fadada samar da tallafin ga karin ma’aikatan da suka cancanta.
A madadin wadanda suka amfana da tallafin, Shugaban ma’aikatan dake share-share na Karamar hukumar Mista Bulus Zamaya ya nuna godiya tare da bayyana karimcin a matsayin na daban kuma wanda aka samar daidai lokacin da ake bukata.
Ya hori wadanda suka amfana da tallafin da su kasance basu yi kasa a gwuiwa ba wajen gudanar da aikinsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *