Wata Jarumar Fim Tonto Dikeh ta roki iyaye da su kasance masu kwarin gwuiwar maida ‘ya’yansu makaranta

Wata Jarumar Fim Tonto Dikeh ta roki iyaye da su kasance masu kwarin gwuiwar maida ‘ya’yansu makaranta sanadiyyar komawa hutu da aka yi.
Jarumar wadda a halin yanzu ta rikide’yar siyasa, ta ba iyaye wannan shawarar ce a shafinta na Instagram, inda tace canza sabon aji ga dalibi wani muhimmin al’amari ne ga yaro.
Ya kara da cewar wasu lamurra sukan zo ne da canjin tsarin jiki ga kuma karuwar dawainiyar gida, sannan ta karfafa gwuiwar iyaye da su rika jurewa ta hanyar yin bakin kokarinsu ta fuskantar aikinsu.
Jarumar ta kuma yi addu’a ga iyayen dake fafutikar maida’ya’yansu makaranta da samun nasarar abin da za su dauki dawainiyar gida da kuma ta yaransu a makaranta.
Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya ya ruwaito cewar Jaruma Dikeh itace a halin yanzu mai rufawa dan takarar kujerar Gwamnan jihar Ribas baya a inuwar Jam’iyyar ADC a zaben 2023.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *