Hukumar kula da Shirin Matasa masu yi wa kasa hidima a jihar Kano ta fara gudanar da shirin kula da lafiya ga al’umar karkara

A ranar Talata ce Hukumar kula da Shirin Matasa masu yi wa kasa hidima wato NYSC a jihar Kano ta fara gudanar da shirin kula da lafiya ga al’umar karkara a Kauyen Farin Ruwa dake yankin Karamar hukumar Shanono dake jihar.
Babbar Jami’ar kula da Shirin NYSC ta jihar Misis Tata Muhammad, wadda ta bayyana haka a lokacin da take kaddamar da shirin, ta bayyana cewar Shirin ya samo asali ne daga Shirin Kula da lafiyar jama’a a yankunan karkara,wato NYSC’s Health Initiative for Rural Dwellers (HIRD) a Turance.
Tace shirin kula da lafiyar da za a gudanar kyauta, na da nufin inganta rayuwar al’ummar dake yankunan karkara, domin su rika samun ingantattar kula da lafiyarsu kyauta.
Shugabar ta kara da cewar matasa masu yi wa kasa hidima dake akwai a sashen na HIRD sune ke gudanar da aikin bincikar rashin lafiyar da samar da magani hadi da samar da gilashin ido ga masu lalurar idanu da kuma sauran lalurorin da suka shafi lafiyar dan Adam.
A cewarta, tun lokacin da aka fara gudanar da shirin, an sami fiye da mutane miliyan biyu da suka amfana da Shirin a fadin kasar nan.
Daga nan sai ta bayyana cewar Shirin ya bada tallafin kekukan guragu guda 300 tare da abokan hulda.
Da yake jawabi a wajen bikin, Dan Majalisar Tarayya dake wakiltar Mazabar Bagwai da Shanono Alhaji Yusuf Badau, wanda Alhaji Sanusi Umar ya wakilata, ya yaba da kokarin Matasa masu yi wa kasa hidima dake gudanar da shirin, sannan ya bada tabbacin goyon baya tare da bada tashi gudunmuwar domin ingantuwar rayuwar al’ummar Mazabarshi.
A jawabansu daban-daban, wadanda suka amfana da Shirin, Adamu Buba da Zainab Musa, sun nuna godiya tare da yi wa Shirin NYSC addu’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *