Majalisar Dattawa za ta rage yawan harajin shigowa da kaya daga waje da aka kudurta a kan Naira Tiriliyan 19.76 cikin kasafin kudin 2023 dake da gibin Naira Tiriliyan 12.4.
Shugaban Kwamitin Kudi najalisar Sanata Solomon Adeola waneda ya bayyana hakan ranar Talata a wajen wani taron musayar ra’ayi a Abuja, yace Majalisar zata rage Naira Tiriliyan 6 da aka kudurta a matsayin harajin shigowa da kaya daga waje ga kamfanoni a 2023 zuwa 2025.
Adeola yace rage yawan harajin ya zama wajibi ganin gibin dake akwai a kasafin kudin 2023 ga kuma dambarwar da tattalin arzikin kasar nan ke fama da ita.
Ya jawo hankali a kan cewar sai an zage damtse wajen rage yawaitar samun gibi a kasafin kudin kasar nan, ya ci gaba da cewar bai kamata a bari ana ciwo bashi ba, ba tare da yin binciken kwakwaf ba.
Shugaban Kwamitin ya bada shawarar da a bullo da wata dubara cikin gaugawa da za a iya lalubo dubarun inganta tara kudaden shiga tare da toshe duk wasu matsalolin durkusar da hanyoyin tara kudaden shigar.
Daga nan sai ya yi kira ga Ma’aikatar Kudi ta tarayya da ta sanya wasu kamfanonin gwamnati guda 63 su zamo masu tara kudaden shigar da zasu rike kansu da kansu ba tare da bata wani lokaci ba.
A bayaninta game da tsarin kashe kudade na ganeren zango da kuma tsarin kashe kudaden da aka shirya yi na 2023 zuwa 2025, Ministar Kudi Zainab Ahmed ta bayyana cewar an yi hasashen Naira Tiriliyan 6.34 ne a matsayin kudaden shigar da gwamnatin tarayya zata samu a 2023.
A cewarta, za a sami Naira Biliyan 373.17 daga bangaren Mai, yayin da za a sami cikamakin Naira Tiriliyan 5.97 daga sauran kafofin da ba na Mai ba.
Ta bayyana cewar akwai bukatar a kara bunkasa hanyoyin tara kudaden shiga da dakile dabi’ar samun gibi a kasafin kudin kasar nan da aka gada a tsarin.