Zaben 2023:zamu samar da Kuri’a Miliyan 15 – Atiku Gida -gida

Zaben 2023:zamu samar da Kuri’a Miliyan 15 – Atiku Gida -gida

Daga Abdullahi Alhassan Kaduna,

Ganin yarda zaben shekara ta 2023 ke kara karatowa, shugaban kungiyar Atiku Gida-gida,wato Atiku door to door mobilization forum,a turance Ambassada Imran Abdullahi.

Yace ƙungiyar su ta lashi takobin samarwa Atiku Abubakar kuri’a har miliyan goma sha biyar a fadin kasar nan,da aka tambaye shi ko yaya zai yi ganin cewa a kwai sauran jamiyu sai yace “munada mambobi da suka kai Kimanin dubu a shirin a fadin kasar nan.

Wanda a halin yanzu mambobin mu sun dukufa wajen wayar wa jama’a kai da muke zuwa gida -gida da zummar wayar musu da kai kan kudorori da manufofin shugaban ƙasa mai zuwa in Sha Allahu wato Atiku Abubakar, fidda Najeriya na halin da take ciki, wanda ya kudurci zai hada kan yan Najeriya.

Shugaban kungiyar yana wan nan jawabin ne a taron kaddamar da mambobin kungiyar reshen jihar Kaduna.

Inda ya kara da cewar su suna goyon bayan shi ne saboda kudirin shi ne na bawa Matasa kaso 40 na mukamai ga matasa ldan Allah ya ida nufi.

Shi kuwa a nashi jawabin shugaban kungiyar Atiku village to village, to kauye zuwa kauye,Abdulbasid Gaini cewa yayi sun dukufa wajen wayar yan Najeriya kai, musamman ma mutanen kauyuka kan kudirin Atiku na samar da tsaro a yankunan karkara, ka san cewar mutanen karkara su noma da kiwo suka sani wanda a halin yanzu babu tsaro a yan kunan su.

Ya kuma kara da cewa manufofi na Atiku Abubakar kan matasa ne yana muke goyon bayan shi na zama shugaban ƙasa,”ka dai ga mu matasa ne,amma muna mara masa baya ,na ganin ya zama shugaban kasar nan,In Allah ya yarda.

Shugaban kungiyar ya kara cewar muna fatan Atiku zai samar da tsaro a yankunan karkara da zai bama yan’uwan mu damar aikin su na noma da kiwo ba tare da fargaba ba ,kamar yarda ake ciki yanzu haka musamman ma yan kunan kasar nan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *