Yansanda a Jihar Ondo sun cafe Matashi da Sassan Jikin Bil Adama

Rundunar ‘Yansandan jihar Ondo ta cafke wani matashi Olaolu Falowo dan kimanin shekaru 26 a kan zargin samunshi da sassan jikin bil Adama.
Jami’in hulda da Jama’a na rundunar SP Funmilayo Odunlami ya bayyana haka a lokacin da rundunar ta baje kolin wasu da ake zargi da aikata miyagun laifuka a ranar Talata.
SP Odunlami yace Falowo mazaunin Kauyen Kuseru a Karamar hukumar Odigbo a jihar, ya taba zama a kurkukun ‘Yansanda a kan zargin satar mota.
Odunlami yace yayin da Falowo ke cikin kurkuku wani ya kai rahoto ga ‘Yansanda cewar wani mummunan wari na fitowa daga dakin Falowo, bayan ‘Yansanda sun bincika gidanshi, sun gano kafafuwan mutum da kuma makamai. Hala kuma an gano kokon kan mutum a cikin wani buhu a gidan manaifin matashin.
Jami’in hulda da Jama’a’ar ya bayyana cewar yayin da aka tuhumi Falowo, yace sassan jikin mutum da aka gani na wani mahaukaci ne da ya gani a cikin daji, ya kuma kashe shi tare da daukar sassan jikinshi, domin ya rabashi da wanalar da yake yi, inda wani dan gidansu ya karyata tare da cewar ba mahaukaci bane manomi ne kuma lafiyarshi kalau.
SP Odunlami yace Falowo da mahaifinshi na tsare a wajen’Yansanda kuma za a kaisu Kotu bayan an kammala bincike.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *