Zulum ya kai Ziyarar Bazata Asibitin Bama

A ranar Litinin ce Gwamna Babagana Umara Zulum ya kai wata ziyarar ba-zata ga Babban Asibitin Bama, domin ganewa idonshi yadda ake kula da lafiyar jama’a.
Gwamnan ya isa Asibitin ne da misalin karfe 10:00 na dare a lokacin da ya isa garin Bama daga Maiduyguri.
Gwamna Zulum dai ya saba kai irin wannan ziyara ga manyan asibitoci da cibiyoyin kula da lafiya da dare, yayin da yafi ziyarar makarantu da sanyin safiya domin ganewa idonshi abubuwan dake faruwa tare da kama ma’akatan da basu dauki aikin da muhimmanci ba.
A Babban Asibitin garin Bama, Gwamnan ya nuna jin dadi a kan yadda ya iske jami’an Nas-Nas da kuma Likitan dake aiki a lokacin Mista Olugbenga Aina wanda shine ma ya kewaya da shi Asibitin domin ganin yadda ayyukan kula da lafiya ke gudana.
Bayan ya kammala duba Asibitin, Zulum ya bukaci Likitan da kuma jami’an Nas-Nas din su yi mashi bayani a kan matsalolin da Asibitin ke fuskanta.
Gwamnan da kanshi ya lura cewar na’urorin sanyaya dakuna da fankoki a dakunan kwantar da majinyata na da matsaloli, yayin da tsarin samar da hasken lantarki mai amfani da karfin hasken rana na bukatar a daga darajarshi.
Don haka nema ya umurci hukumar gudanarwar Asibitin da ta hanzarta shirya rahoton abubuwan da ake nema nan take, su aika mashi ta hannun Kwamishinan Lafiya na jihar Farfesa Mohammed Arab.
Gwamnan ya kuma sanar da samar da guraben aiki nan take ga ‘yan garin Bama wadanda suka mallaki takardun shaidar kammala karatun aikin Likita ko hadagunguna ko kuma Nas-Nas domin kara yawan jami’an lafiya a Babban Asibitin da kuma Cibiyoyin kula da lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *