Gwamna Zulum ya Ziyarci Garin Bama

Zuwan Gwamna Babagana Umara Zulum garin Bama domin gudanar da wasu ayyukan jin kai da na raya kasa, ya kai gaisuwar ban girma ga Shehun Bama Umar Ibn Shehu Kyari Ibn Umar El-Kanemi a fadarsa.
Jim kadan bayan da Gwamnan ya duba wani wuri inda ke sa ran dubban ‘yan yankin zasu karbi tallafin jin kai.
Tsakanin ranakun Litinin da Talata, ya duba aikin raba katunan cancanta ga wadanda zasu karbi tallafin jin kan.
Gwamna Zulum ya kuma gudanar da taruka daban-daban da masu ruwa da tsaki a Jam’iyyar APC a garin Bama, ana kuma sa ran zai gana da shugabannin al’umma a lokacin zaman da zai yi a Bama.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *