Rundunar Yansandan Jigawa ta tabbatar da mutuwar jariri dan kimanin wata bakwai da kuma wasu mata sana diyyar kifewar kwale kwale

Rundunar ‘Yansandan jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar wani Jariri dan kimanin wata bakwai da kuma wasu mata guda hudu sanadiyyar kicewar wani kwale-kwale a Karamar hukumar Guri.
Jami’in hulda da Jama’a na rundunar ‘Yansandan jihar DSP Lawal Salisu ne yatabbatar da hakan ranar Laraba a garin Dutse.
DSP Salisu ya bayyana cewar a ranar Talata da misalin karfe 6 na yamma suka sami rahoton cewar da misalin karfe 4:30 na yamma wasu mata guda hudu da wani Jariri sun hau wani kwale-kwale daga garin Nguru jihar Yobe zuwa Kauyen Adiyani Karamar hukumar Guri ta jihar Jigawa.
Amma abin bakin ciki kwale-kwalen ya kife kusa da inda zasu je, amma direban ya tsira da ransa yayin da su kuma suke nutse.
Ya bayyana cewar dandanan direbobin dake yankin suka yi kokarin ceto fasinjojin kwale-kwalen, inda daga bisani suka gano gawarwakinsu.
Jami’in hulda da Jama’ar yace an kai gawarwakin Asibitin garin Adiyani inda Likitan Asibitin ya tabbatar da rasuywarsu.
Yace sunayen wadanda suka mutun sun hada da Oneyaniwura Kasagama ‘yar kimanin shekaru 50 da Lafiya Bulama ‘yar shekaru 40 da Badejaka Kasagama shekaru 40 da Gimto Kasagama shekaru 40 da kuma Jariri dan wata bakwai Mai Madu Bulama.
DSP Lawal Salisu yace dukkansu ‘yan Kauyen Adiyani ne, ya kara da cewar an fara bincike a kan musabbabin faruwar hakan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *