Babban Hafsan Sojojin Najeriya Leftana Janar Faruk Yahaya yace rundunar sojojin kasar nan ta lashi takobin kawar da ta’addanci da sauran munanan ayyukan

Babban Hafsan Sojojin Najeriya Leftana Janar Faruk Yahaya yace rundunar sojojin kasar nan ta lashi takobin kawar da ta’addanci da sauran munanan ayyukan dake barazana ga harkar tsaro a kasar nan.
Ya bada tabbacin hakan ne yayin da yake gabatar da wata ga jami’an sojin da suka kammala kwas na 45 a Kwalejin horas da manyan jami’an soji dake Jaji.
Janar Yahaya, wanda ya jaddada kwarewar aiki da jajircewa ta fuskar gudanar da aikin soji dake gudana a halin yanzu, ya yi alkawarin jajircewar rundunarsa wajen ci gaba hada hannu da sauran hukumomin tsaro da kuma masu ruwa da tsaki.
Don haka nema Babban Hafsan yace muradinsa shine kokarin cimma ka’idodin da kundin tsarin mulki ya gindaya a kan sojojin Najeriya.
A jawabinsa, Kwamandan Kwalejin AVM Oluwarotimi Tuwase ya hori mahalarta horon da su sanya muradin Babban Hafsan a zuciyarsu wajen yaki da matsalar tsaro a kasar nan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *