KWAMISHINA A JIHAR YOBE YA RASU A HADARIN MOTA

KWAMISHINA A JIHAR YOBE YA RASU A HADARIN MOTA

Kwamishinan matasa da wasanni a jihar Yobe Alh Goni Lawal ya rasu.
Mai magana da yawun ma’aikatar Tijjani Chiroma ne ya tabbatar da labaran rasuwar.
Ya ce Lawal Dan shekaru 57 ya gamu da ajalinshi ne sakamakon hadarin mota a kan hanayar shi daga Potiskum zuwa Azare da misalin karfe 7:30 na marecen Talata.
Ciroma ya ce marigayon na kan hanyar shi ta zuwa Kano inda zai hau Jirgi zuwa Abuja dan wani aiki.
An dai nata shi Kwamishina ne a shekarar 2019, kuma yayi Dan majalisar wakilai a shekarun 2007 zuwa 2015..
Ya rasu ya bar Mata biyu da yara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *