AN BUKACI JAMI’AN TSARO SU SANYA KISHIN KASA
Mai rikon mataimakin babban kwamanda mai kula da ayyika a hukumar tsaro ta farin kaya da aka fi sani da Civil Defence ACG Muhammal Lawal Haruna ya bukaci jami’an hukumar a jihar Kaduna da su rika nuna kishin Kasa a yayin gudanar da aikin su.
Muhammad Lawal yayi wannan kiran ne yayin hira da manema Labarai Jim kadan bayan ya gama ziyarar duba ma’aikatan hukumar a Kaduna, ya na mai fadakar sa su da su maida hankali wajen kula da rayuka da dukiyoyin al’umma.
Daga nan sai Haruna ya bukaci su kuma yan Kasa da su rika taimaka ma ma’aikatan ta hanyar basu bayanai da zasu taimaka wajen kama bata gari.
Kwamandan ya kara da cewa Civil Defence a shirye suke su yi aiki da duk wani ko wata hukumar da zata tallafa a rage aikin ta’addanci.
Ya ce “ku duba ku gani ba mu da wata bariki cikin ku muke dan mu yi aiki da ku”.
Tun a darko a nashi jawabin maraba kwandan jiha na Civil Defence din a jihar Kaduna IDRIS Yahaya Adah yace hukumarar ta horar da Jami’an ta da dama ta yadda za su gudanar da aiki.
Ya ce to ga shi yau kuma mataimakin babban kwamandan ya kawo masu ziyara dan ya ga yadda suke tafiyar da ayyukansu.