FIYE DA MUTANEN AREWA DUBU DARI BIYU SUKA AMFANA DA TALLAFIN GWAMNATIN TARAYYA.

FIYE DA MUTANEN AREWA DUBU DARI BIYU SUKA AMFANA DA TALLAFIN GWAMNATIN TARAYYA.

Karamar Minister Masana’antu Hajiya Maryam Katagun tace kimanin Mutane 237,138 ne suka amfana da tallafin gwamnatin tarayya na kanana da matsakaitan Sana’o’i a yankin Arewaci maso yammacin Najeriya.
Tallafin dai ana raba shi ne ga masu kanana da matsakaitan Sana’o’i da zummar rage masu radadin matsalar da aka sha likacin hana zirga zirgar Kurona (COVID-19).
Maryam Kaltungo na wannan bayanin ne a Kano yayin wata ganawa da Wadanda suka amfana da tallafin.
Ta ce tallafin dai ya kasu ne kashi biyar da kuma da dama sun amfana da kowane kashi.
Kaltungo wadda ta samu wakilin babban darakta mai kula da hukumar bada tallafin na Kanana da Matsakaitan Masana’antu SMEDAN Mr Wale Fasanya tace shirin wani bangare ne na tallafa ma jama’a masu kananan Sana’o’i da COVID-19 ta kassara.
Ta ce shirin ya kuma baiwa Mata da masu bukata ta musamman muhimmanci tare da basu kashi Arba’in da biyar dan su ma a dama da su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *