AN JA KUNNEN SARAKUNA A JIHAR BAUCHI

AN JA KUNNEN SARAKUNA A JIHAR BAUCHI

Gwamnan jihar Bauchi ya ja kunnen masu sarautun gargajiya da jami’an tsaron da ake hada baki da su wajen baiwa yan bindiga masu tayar da kayar baya mafaka ko bayanai.

Gwamna Sanata Abdulkadir Bala Muhammed, ya wannan Jan kunne ne a garin Duguri, lokacin da ya ke ci gaba ziyarar jajantawa al’umomin da aka kashe ma ‘yan uwa dama wadanda aka sace domin kudin fansa.

A jihar ta Bauchi kididdiga na nuni da cewar, ana samun yawaitar kashe kashen mutane da kuma sace su, daga yan bindiga a sassan jihar, musamman a yankunan kananan hukumomin Alkaleri da Tafawa Balewa da kuma Ningi.

Yayin da ‘yan bindiga ke cin karensu ba bu babbaka, wanda a tsakanin watan Yuni da Yuli an kashe mutane fiye da goma, an kuma sace mutane 17 don kudin fansa,

Rahotanni a yanzu haka dai na nuna cewar wasu daga cikin ‘yan uwan wadanda aka sace sun biya kudi sun karbo mutanensu.

A jawabinsa, Gwamna Bala Abdulkadir, ya bayyana alhini game da abubuwan dake faruwa na bakin ciki a jihar, sannan ya ci gaba da cewa suna da labarin masu taimakawa ‘yan bindiga dake zaune a cikin duwatsun dake wajen gari, amma yanzu ya bada umarnin a kama duk wanda ke da hannu.

Da yawan al’umomin yankunan na ci gaba da mika kukansu ga shugabanni tare da rokon Allah ya sawwake mu su wannan tashin hankali dake addabarsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *