KWAMISHINAN HUKUMAR ZABE A KATSINA YA BAYYANA MATSALAR TSARO AKAN RASHIN YIN KATIN ZABE
Kwamishninan Hukumar Zabe a Jihar katsina Alhaji Jibril Ibrahim Zarewa ya bayyana matsalar rfufe layin wayoyin da akai a jihar a matsayin abun da ya ja za aka samu matsalar rashin yawaituwar katin zabe.
Jiobrin Zarewa na wannan bayanin ne ga manema labarai a ofisdhin shi dake a katsina.
Ya ce rufe la hanyoyin sadarwar da akai da zummar samar sauki ga matsalar tsaro ya kuma haifar da matsalar samar da bada katunan zaben a wasu yankunan jihar. Inda ya kara da cewa rufe wadannan kananan hukumomi 17 ya kawo matsalar ga kusan rabin kananan hukumomin jihar zarewa ya bayyana cewa jihar katsina kamar wasu jihohin makwabtan ta irin su Kaduna, Zamfara, Sokoto da Niger na fama da irin wannan matsala ta rashin tsaro.
Kwamishinan zaben y ace tun da a lokacin gwamnati ta rufe hanyoyion sadarwa a wannan kananan hukumomi hakan su ma ya sanya dole su ka dakatar da gudanar da aikin bada katin zaben a yankunan.
Ya kara da cewa dakatar da aikin a wadannan kananan hukumomi 17 ya sanya aikin bada katin ya shafi kusan rabin kananan hukumomin jihar da su ka hada Jibia, Batsari, Kurfi, Dutsinma, Dan Musa, Safanma, Matazu, Musawa, Malumfashi, Kafur, Danja, Sabuwa, Bakori, Funtua Faskari da Dandume da Kankara.
To sai dai yace a yanzu gwamnati ta yi kokari wajen ganin an samu karuwar yadda ake rajistar. Inda kuma yay aba ma kokarin masarautun Katsina da daura ta yadda suka baiwa Hakimai da sauran masu rike da sarautun gargajiya umurnin a kara fadakar da jama’a kan yin rajistas katin zabe.
Zarewan yace hakan kuma yasa cikin sati guda sun ga Karin yadda ake tururuwar zuwa wajen yin katin zaben.