Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ba da tabbacin cewa, jinin yarinya ’yar shekaru 5 Hanifa da malamin makarantar su Abdulmalik Tanko ya yi wa kisan gilla, ba zaya tafi a banza ba.
A matakin farko, gwamnatin ta rufe makarantar da wancan malamin ke jagoranta, wato NOBLE KIDS don gudanar bincike.
Kwamishinan yada labaru na jihar Kano Muhammad Garba, ya ba da sanarwar cewa, tabbas gwamnti za ta tabbatar da an hukunta wanda ya yi kisan.
Malamin Abdulmalik Tanko wanda ya sace Hanifa, ya karbi kudin fansa, sannan ya kashe ta, ta hanyar sanya ma ta guba, ya na hannun ‘yan sanda inda bayan kammala bincike za a gurfanar da shi gaban kotu tare da wadanda suka aikata wannan mugun aiki.
Kisan gillar Hanifa, ya jawo matukar takaici da bacin rai tsakanin dukkan ‘yan Najeriya inda a ka yi ta yada hotunanta da mika ta’aziyya.