ZANGA ZANGAR NLC: MALAMN ASUU SUN YABA

ZANGA ZANGAR NLC: MALAMN ASUU SUN YABA

Sakamakon gangamin da Kungiyar Kwadago ta Kasa NLC ta fara yau Dan nuna goyon bayanta ga yajin aikin malaman Jami’a ASUU wasu malaman Jami’ar sun yaba.
Dr ISA Ibrahim daga tsangayar sashen jarsunan Afirka a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zaria ya sheda ma ABC Hausa cewa suna maraba tare da yabawa da sannan baici da Kungiyar Kwadago take ma su.
Dr Ibrahim Wanda ya xanta ba ABC ta wayar tafi da gidanka yace Kungiyar Kwadago a matsayin ta na uwa ga dukkan kungiyoyi dama tuni ya kamata ta yi haka.
Shi wani malamin daga Jami’ar Bayero Ta Kano Dr Mustapha Kallamu ya bayyana Farin cikin shi da wannan kokari na NLC yana mai fatan hakan zai kawo daukar mataki daga gwamnatin tarayya na ganin an kawo karshen yajin aikin.
ABC Hausa ta samu jin ra’ayin Malama Maryamojammad daya daga cikin ma’aikata da ba na koyarwa ba Wadanda suma suna cikin yajin aikin, inda ta ce su dai fatan su gwamnati ta dubi halin da dalibai suke ciki da kuma na yadda su ma ma:aikatan masu koyarwa da Wadanda ba.su koyarwa su ke ciki kasancewa ba a biyan su Albashi na tsawon watanni.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *