KAMFANIN MU BA NA ATIKU BANE

KAMFANIN MU BA NA ATIKU BANE

Hukumomin gudanarwar kamfanin Mikano ma su injinan Mikano sun ce ba su da wata alaka da Dantakarar shugaban Kasa Atiku Abubakar.
A wata sanarwa da kamfanin ya fitar ga manema Labarai ya sheda cewa akwai maganganu dake yawo cewa kamfanin na Dantakarar Shugaban kasar ne.
Sanarwar wadda Manajan Daraktan kamfanin Firas Mamlouk ya sanya ma hannu ta ce babu wani hadi da ke tsakanin kamfanin da Maigirma Atiku Abubakar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *