HUKUMAR ICPC TA SHIGAR DA MAGATAKARDAR KOTU A KOTU
Hukumar dake kula da zarniya da almundahana da sauran ayyukan assha da suka shafi ma’aikata ICPC ta gurfanar da wata babbar mataimakiyar magatakardar babbar kotun tarayya dake Fatakwal kotu.
A wata sanarwa da maimagana da yawun ICPC din Azuko Ogongo Monday ta fitar tace an gurfanar da Mrs Nkem Nmba ne bisa zargin laifuka guda uku a wata babbar kotun tarayya ta 12 dake a Fatakwal din.
A cewar sanarwar daya daga cikin zargin da ake ma Mrs Nmba harda zargin amsar wasu kudadr N500,000 ta hanyar asusun ta daga wani kamfanin gas.
Mrs Nmba dai tace kudin nata ne kuma suna cikin wasu kaso ne na hakkinta.
Wadda ake zargin dai ta ki amsa ko da laifi daya a zargin da ake mata.