MATAIMAKIN SHUGABAN KASA YA GODEMA YAN NAJERIYA

MATAIMAKIN SHUGABAN KASA YA GODEMA YAN NAJERIYA

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osibanjo ya mika sakon godiyar shi ga yan Najeriya a irin addua’oin da sukai ta mashi.
A wata sanarwa da mataimaki na musamman na mataimakin shugaban kasar a fannin yada labaru da hulda da Jama’a Laole Akande ya sa ma hannu yace addu’o’in yan kasar sun taimaka wajen samun saukin shi.
Mataimakin shugaban kasar ya kuma gode ma tawagar likitoci da ma’aikatan da sukai mashi aikin Tiyatar akan irin namijin kokarin da su ka yi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *