WATA BABBAR MOTA TA FADA KAN WASU MOTOCI
Hukumar kula da rage afkuwar haddura da aka fi sani da Road Safety sun bayyana cewa wata mota Trailer ta fada kan wasu motoci bakwai dake tafiya a Jos.
Jami’in hulda da jama’a da wayar masu da kai na hukumar a jihar Plateau Peter Longsan shi ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar.
Longsan yace hadarin da ya faru bakin kofar makarantar Hillcrest sakamakon kin bin ka’idar tsarin rage tuki da aka saka a wurin.
Yace Mutane uku sun ji rauni inda aka dauke su zuwa Asibitin kwararru dan basu cikakkar kulawa.
Longsan daga nan sai ya shawarci masu tuki da su tabbatar suna kula da lafiyar ababen hawan su domin kauce ma faruwar irin hakan.