YAN SANDA A ZAMFARA NA TSARE DA DAN JARIDA

YAN SANDA A ZAMFARA NA TSARE DA DAN JARIDA

Rundunar Yansanda a jihar zamfara sun tsare wani Dan Jarida Umaru Maradun wakilin Jaridar leadership.
Kwamishinan yan sandan jihar Ayuba Elkannah ya tabbatar ma shugaban kungiyar yan jaridu na jihar Ibrahim Maizare a wata tattaunawa ta wayar tarho.
Elkannah yace zai duba matsalar kafin daukar wani mataki.
An dai kama Umaru Maradun a garinsu na Maradun mahaifar Gwamnan jihar da sanyin safiyar Asabar inda kuma aka yo Gusau da shi sashen Binciken rundunar yansandan na CID.
To amma duk da shugaban kungiyar yan jaridun ya jagoranci wata tawagar yan jaridun Dan zuwa hedikwatar yan sandan Dan neman belin Maradun abun ya gagara.
Yanzu haka dai Maradun din na garkame a sashen Binciken ma CID a.Gusau.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *