AN NADA MATAIMAKIN SHUGABAN JAMI’AR FUDMA MAMBA NA MAAUN
An nada mataimakin shugaban Jamiar Gwamnatin Tarayya dake Dutsinma FUDMA a matsayin mamba na hukumar gudanarwa Jami’ar Maryam Abacha American University dake nan Najeriya.
A wata sanarwa da Jami’in yada labaru na FUDMA Habibu Aminu Umar ya sa ma hannu tace nadin na Farfesa Bichi ya biyo bayan zaman da Kwamitin Amintattu na Jami’ar yayi a watan Fabrerun wannan shekara.
A cikin sanarwa, Mamallaki kuma shugaban Jami’ar ta Maryam Abacha Farfesa ADAMU Abubakar Gwarzo Wanda ya taya Bichi murna ya kuma ce zaben shi ya biyo bayan kwakkwaran bincike da da wasu manyan Mutane su ka yi inda suka samo mai himma da kwazo da son ci gaban Ilimi da ma na Dan Adam kafin nada shi wannan mukami