SARAKUNAN KATSINA DA DAURA SUN SHAWARCI AL’UMMOMINSU KAN RAJISTAR ZABE

SARAKUNAN KATSINA DA DAURA SUN SHAWARCI AL’UMMOMINSU KAN RAJISTAR ZABE

A yayin da ake gab da rufe aikin yin rajistar katin zabe, Sarakunan Katsina Dr Abdulmumin Kabir Usman da na Daura Dr Umar Faruk Umar sun shawarci Juma’ar su da su gaggauta yin katin zaben.
Da yake hira da manema Labarai a fadar shi ciki hada ABC Hausa, Abdulmumin Kabir yace yin rajistar katin zaben na da matukar muhimmanci musamman ga matsa Wadanda a yanzu suka cika shekaru 18 da haihuwa.
Sarkin na Katsina ya bayyana cewa muhimmancin yin katin zaben ba kawai ga yan siyasa ko masu yin zabe ba, kasancewa ana iya amfani da shi wajen gane yawan al’ummomi da yadda za a taimaka masu.
Shi ma a nashi jawabin na daban a fadar shi da ke Daura, Sarkin na masarautar Daura Dr Umar Faruk ya jaddada muhimmancin yin katin zaben.
Sarkin na Daura ya ce baya ga nuna yawan jama’a a siyasance ana iya amfani da katin zaben wajen tallafa ma jama’a ta fuskar bunkasa rayuwa ta la’akari da yawa ko irin yawan kuriar da yanki ya bada.
Dukkan sarakunan dai sun yaba da kokarin gwamnatin jihar Katsina wajen fadakar da al’umma kan a tashi a yi rajistar katin zaben.
Sun kuma ce shawara, gargadi da ma rokon da su ke ma al’umma na su fita su yi rajistar katin zaben sai gaba za su ga amfanin hakan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *